27 Mayu 2021 - 12:53
​Isma’il Haniyya Ya Gode Wa Qatar Kan Ware Dala Miliyan 500 Domin Gyaran Yankin Zirin Gaza

Shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya gode wa gwamnatin kasar Qatar kan ware dala miliyan 500 domin gyaran yankin zirin Gaza da Isra’ila ta rusa.

ABNA24 : A cikin wani bayaninsa da ya fitar a daren jiya, Shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, matakin da kasar Qatar ta dauka na ware dalar Amurka miliyan 500 domin gyara Gaza, sakamakon barnar da gwamnatin yahudawan Isra’ila ta yi wa al’ummar yankin, da cewa hakan abin yabawa ne.

Ya ci gaba da cewa matakin na Qatar bai takaita da gyaran Gaza ba, domin kuwa a tsawon shekarun da Gaza ta yi a killace, Qatar tana bayar da taimako ga al’ummar yankin, wanda kuma hakan abin yabo ne kuma abin koyi.

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al Thani ya sanar a yammacin jiya cewa, bisa umarnin sarkin Qatar, gwamnatin kasar ta ware dala miliyan 500 domin sake gina yankin zirin Gaza.

A cikin bayanin da ya rubuta a shafinsa na twitter, ministan harkokin wajen kasar ta Qatar ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kare hakkokin al’ummar falastinu, tare da bin dukkanin hanyoyi na diflomasiyya, domin ganin an yi adalci wajen bai wa Falastinawa damar kafa kasarsu mai cin gishin kanta.

342/